An Kammala Taron Horas Da Matasa Akan Yadda Zasu Samu Kudu Ta Hanyar Wayar Hannu Wanda KVC Katsina Ta Shirya.
Daga: Muhammad Ali Hafizy. | Katsina Times.
A yau Laraba 10 ga watan Satumba 2025, aka kammala taron da aka shafe tsawon kwanaki uku ana horas da matasa akan hanyoyin da zasu bi domin samun kuɗi ta wayoyin hannu su, wanda Katsina Vocational Training Center haɗin gwiwa da Paracha Family Abuja suka shirya.
A rana ta karshe, taron ya yi duba akan yadda mutum zai yi kasuwanci a cikin manhajar Wasaf (Whatsapp Business), sannan kuma an bayyana ma mahalarta taron yadda zasu kyautata kasuwancin su, da kuma hanyoyin da zasu bi na saye da sayarwa a cikin manhajar.
Malam Mubarak daga jihar Jigawa masanin hanyoyin daban na samun kuɗi ta wayar hannu, wanda shi ne ya jagoranci koyar da matasan na tsawon kwanaki uku, ya tunatar da matasan akan muhimmancin yin sana’a ko yaya take domin gujewa zaman banza.
Ya kuma yi bitar bayanan na yayi masu na kwanakin da suka gabata, tare da amsa tambayoyin su na abubuwan da suka shige masu dubu, tare da yi masu karin haske akan duk abin da basu gane ba, ko kuma wani abu da suke san sanin yadda yake.
Daga ƙarshe baban alkali na jihar Katsina Justice Musa Danladi Abubakar shi ne na rufe taron da jawabin shi, a inda ya yaba ma matasan, tare da shawartarsu akan su kiyaye yin abubuwan da suka saba ma addini da wayoyin su, sannan kuma su yi kokari wajen aikata abubuwan da aka koyar dasu na samun kudin.
Ya kuma jagoranci bayar da shaidar halartar taron gare su, tare da yin fatan alkairi ga dukkanin su.








